Zelensky zai gana da Trump domin sanya hannu kan yarjejeniyar haƙar ma'adinai

Zelensky zai gana da Trump domin sanya hannu kan yarjejeniyar haƙar ma'adinai

Karo na farko kenan da shugabannin biyu za su gana tun bayan da Trump ya yi gaban kansa wajen fara ganawa da Rasha da zummar kawo ƙarshen yaƙinta da Ukraine.

Tuni dai shugaba Trump ɗin da Zelesnkyy suka cimma matsayar amincewa da yarjejeniyar da za su sanya wa hannu a yau, wadda a ƙarƙashinta Amurka za ta mallaki wani kaso mai tsoka na ribar haƙo ma’danan ƙarƙashin ƙasar da Ukraine ta mallaka,, lamarin da ke zama wata sigar biyan Amurka ladan tallafin tsaro na kusan Dala biliyan 66 da ta riƙa bai wa Ukraine a tsawon shekaru uku da ta shafe tana yaƙi da Rasha.

Daga cikin sauran batutuwan da ake sa ran yarjejeniyar za ta kunsa akwai, kafa gidauniyar sake gina Ukraine, wadda gwamnatin ƙasar za ta zuba wa kaso 50 na kuɗaɗen shigar da take samu, yayin da ita kuma Amurka za ta ɗauki nauyin shafe lokaci mai tsawo tana tallafa wa Ukraine ɗin ta fuskar tattalin arziƙi da zaman lafiya, sai dai banda irin tallafin sojin da take ba ta a yanzu.

Ukraine na cikin sahun gaba a tsakanin ƙasashen da suka mallaki ɗimbin arziƙin ma’adanan tama da ƙarafa da kuma Lithium baya ga Man Fetur da Iskar Gas.

Sai dai akasarin ma’adanan ƙarƙashin ƙasar na Ukraine na kwance ne a yankunan da a yanzu suke ƙarƙashin ikon Rasha, wadda bayanai suka ce tuni shi ma shugabanta Vladimir Putin ya yi wa Amurka tayin mallakar wani kaso na ribar haƙo ɗimbin arziƙin a yankunan da ta ƙwace, kuma ga dukkanin alamu shugabannin biyu za su iya cimma matsaya a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)